Revelation of John 10

Malaʼika da Ƙaramin Naɗaɗɗen Littafi

1Sai na ga wani babban malaʼika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta. 2Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa, 3ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana. 4Saʼad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.”

5Sai malaʼikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama. 6Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri! 7Amma a ranakun da malaʼika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”

8Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun malaʼikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.”

9Sai na je wajen malaʼikan na ce masa yǎ ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yǎ yi tsami, amma a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.” 10Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun malaʼikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma saʼad da na cinye, cikina ya yi tsami. 11Saʼan nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, alʼummai, harsuna da kuma sarakuna.”

Copyright information for HauSRK